Kimanin 'yansanda 3500 za'a jibge a kananan hukumomi tara inda za'a gudanar da zaben kujerar yankin Neja ta gabas.
Yankin ya hada da karamar hukumar Suleja wadda ta sha fama da tashin bama bamai a can baya.
Rundunar 'yansandan dai tace ba zata yi kasa a gwiwa ba wurin cafke duk wanda aka samu yana shirin dama lissafin jama'a a lokacin zaben. Kakakin rundunar 'yansandan na jihar Neja Mr. Ibrahim Gambari yace sun yi duk abun da ya wajaba domin ganin an yi zaben cikin lafiya da kwanciyar hankali da kuma tabbatar da adalci.
Ita hukumar zaben Najeriya ko INEC a takaice tace sama da mutane dubu dari tara da tamanin da daya ne zasu kada kuri'a a lokacin zaben.Hukumar tace ta kammala duk shirye-shiryenta da suka wajaba.
Muhammed Madawaki Wasi kakakin hukumar zaben ko INEC mai kula da jihar Neja ya shaidawa manema labarai cewa wasu kayan aikin sun shigo kuma an turasu wuraren da za'a yi aiki dasu. Sauran kayan da suka fi mahimmanci sai nan da kwana biyu ko uku za'a kawosu.
Kungiyoyin siyasa hudu ne suka tsayar da 'yan takara a zaben. Wadanda suka shiga zaben su ne APC da PDP da APGA da SDP.
Shugaban jam'iyyar APGA a jihar Neja Musa Aliyu Liman ya karyata labarin cewa sun shiga zaben ne domin batawa wasu gari. Wasu na zargin cewa PDP ce ta turosu domin su bata ma wasu kuri'a. Wasu kuma sunce PDP ta ce ita ta tsayar dasu. Liman ya kira masu zargin da PDP su fito fili su fadi hakan cewa su ne suka tsayar das ko kuma Allah ya tona masu asiri.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5