Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Nemi Jama'a Su Mika Makamansu

Shugaban Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu

A cigaba da daukar matakan tsaro da rundunar 'yansandan Najeriya ke yi, Sfeto-Janar din 'yansandan Najeriya Mohammed Adamu ya shawarci duk wani mai bindiga ya mika ta ga hukumar kafin ta je karbowa da kanta.

A wani mataki na shawo kan barazanar tsaro, Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya nemi jama'a su mika makamansu ga rundunar ba tare da bata Lokaci ba.

Da ya kewa Muryar Amurka karin bayani, CSP Al-mustapha Sani, na sashin hulda da jama'a na hedkwatar ‘yan sandan kasar ya ce dole ne a mika makami da aka mallaka ta kowacce irin hanya.

Rundunar ‘yan sandan ta ce, duk wanda ya mika makaminsa salin alin, to bai da damuwa; amma duk wanda ya yi kememe ya ki mika makaminsa, kuma aka kama shi to lalle zai yaba wa aya zaki.

Har ila yau rundunar ta ce tuni jami'anta masu leken asiri suka dukufa wajen aiki ta karkashin kasa don daukar mataki kan duk wadanda basu mika makaminsu ba.

Saurari cikakken rahoton daga Hassan Maina Kaina a Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Nemi Jama'a Su Mika Makamansu