Hedikwatar ‘yan Sandan Najeriya ta karyata zargin da gwamnan jihar Rivers Barista Nyesom Wike ya yi na cewa sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya ya umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar Rivers da ya halaka gwamnan.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Jimoh Moshood, yace wannan abin bakin ciki ne ganin yadda irin wannan magana ke fitowa daga bakin gwamna da kansa. Ya ci gaba da cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya tana sanar da cewa maganar da mai girma gwamna Nyesom Wike ya yi ba gaskiya ba ce.
A cewar rundunar ‘yan sandan yanzu haka kimanin jami’an ‘yan sanda 221 ke tsaron lafiyar mai girma gwamnan, kuma bai taba korafin cewa jami’an ‘yan sandan na sakaci ko ganganci da aikin tsaron lafiyarsa ba.
Malamin siyasa a jami’ar Abuja, Dakta Abubakar Umar Kari, na ganin wannan batu ya nuna irin kamari da dangantaka ta yi tsakanin gwamnan jihar Rivers da hukumar ‘yan Sanda, kasancewar shi gwamna na kallon hukumar ‘yan sanda a matsayin ‘yan adawa saboda haka ba sa yi musu adalci, su kuma jami’an tsaro na fadin cewa jihar Rivers ta yi kamari wajen rigingimu da kashe-kashe na siyasa.
Domin karin bayani ga cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5