Tsohon shugaban kasar ne ya shirya taron da nufin kawo sasanci a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar da suka sami rarrabuwar kawuna a tsakaninsu, kwatsam sai hatsaniya ta barke tsakanin Ali Sherrif, da tawagarsa da suka hada da Ahmed Gulak, da Yerima Ngama, da kuma Abubakar Gada, suka fice daga taron.
Sherrif, ya shaidawa manema labarai cewa a matsayinsa na shugaban jam’iyya, ya kamata a bashi dama ya yi magana ko ya jagoranci taron amma hakan ya gagara.
Daga karshe dai Goodluck Jonathan, ya kafa wani kwamiti da zai cigaba da laluben sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar wanda Jonathan zai jagoranta, da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, a matsayin mataimaki.
Sakataren shirye shirye na Ahmed Makarfi, Abdul Ningi, ya bayyana cewa Sherrif, ya hakikance dole sai an kira shi shugaban jam’iyya an kuma bayyana masa cewa ba a kai wannan matsayar ba tukuna, bayan haka ne ya ce shi bazai saurari taron ba idan har baza a kira shi da shugaban jam’iyya ba.
A nasu bangaren, mutane Modu Sherrif sun ce taron badi da wani tasiri kamar yadda tsohon ministan kudi Yerima Ngama, ya bayyana, shugaban kwamitin amintattun PDP Walid Jinrin, ya ce babu shakka jam’iyyar zata farfado.
Nasiru Adamu El-Hikaya na dauke da karin bayani.
Facebook Forum