Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Adamawa Tayi Barazanar Ficewa Daga APC


 Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo
Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo

Gwamnatin Jihar Adamawa Bata Ji Dadin Yadda Gwamnatin Tarayya Bata Tuntubarta Wajen Nade Naden Mukamai Ba.

Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Adamawa Abdulrahman Abba Jimeta ya koka da yadda ake wancakalar da jihar sa wajen nada mukaman gwamnatin tarayya, inda ya ce idan har gwamnatin tarayya batayi komai a kai ba zasu fice daga jam’iyyar APC.

Jami’in gwamnatin ya fadi hakan ne a gaban gwamnan jihar Muhammad Jibrila Bindow, ba tare da ya kwabe shi ba a lokacin da suke ganawa da shugabannin jam’iyyar APC na kasa da suka ziyarci jihar domin zaben cika gurbi na shiyar Arewa Maso Gabas.

Abba Jimeta ya bayyana barazanarsu da cewa, ‘’ Ku gaya musu cewa hakurin mu ya fara cika, musamman ganin cewa basu damu da halin da muke ciki ba, mu ne sojojin jam’iyyar kuma mune ya kamata mu amfana da jam’iyyar amma idan har suka ki yin komai a kai za mu canja sheka zuwa jam’iyyar adawa.

“Gwamnatin tarayya ba ta neman shawaran mu idan za tayi nade-naden ta musamman wanda ya shafi jihar Adamawa.”
Tuni wadannan kalaman suka fara jawo martani da cece-kuce a jihar inda wasu kusoshin jam’iyar ke cewa Allah raka taki gona!

Alh.Muhammadu Iliyasu Gamawa na cikin kusoshin jam’iyar APC a jihar Adamawa ya ce su basu yi mamaki ba,da wannan barazana da kusoshin gwamnatin jihar Adamawa ke yi a yanzu.

To sai dai kuma yayin da aka soma maida martani,gwamnatin jihar tace ba haka batun yake ba,kamar yadda kwamishinan yada labaran jihar Ahmad Sajo yayi bayani.

Wannan ne dai karo na hudu da babban hafsan gidan gwamnatin jihar ke irin wadannan kalamai da kansa gwamnatin jihar lashe amanta.
Ko ma menene dai yanzu lokaci ne kawai ke iya tabbatar da yadda zata kaya kafin nan da shekarar 2019!

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG