ABUJA, NIGERIA - Shirin na OP VELVELT da kwamishinan ‘yan sanda CP Ben Igwe ke jagoranta da kansa, na kai samame da hare-hare ne a maboyar miyagu dake sassa daban-daban na birnin.
A irin wannan samame na baya-bayan nan ne kwamishinan ‘yan sandan ya jagoranci kai samame a wani gidan dambe dake unguwar Dei Dei da ke wajen birnin Abuja inda aka cafke kimanin mutane dari uku.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Abujan ta ce an sami makamai da miyagun kwayoyi daga wurin wasu da ga cikin mutanen da aka kama.
Ta ce za a tantance wadanda ake ganin ko zargin masu laifi ne don daukar mataki na gaba, wanda bai da laifi kuma a sallame shi.
Dama dai mutanen garin yankin sun dade suna korafi da nuna fargabar barazanar tsaro ganin nau'o'in mutanen dake tattaruwa a wannan gidan damben.
Amma masana tsaro irin su Dr. Kabiru Adamu na ganin ko da yake wannan mataki ne mai kyau amma rashin daukar matakan hukunta duk wanda aka samu da laifi a irin wannan mataki ba karamar koma baya bane.
Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5