Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Kaddamar Da Runduna Na Musamman Domin Yaki Da Satar Mutane


Babban Sufeton Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun
Babban Sufeton Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun

A yayin kaddamar da rundunar ta musamman a Abuja, Babban Sufeton ‘Yan Sandan yace rundunar ta kunshi zaratan ‘yan sandan kwantar da tarzoma da suka sami horo na musamman domin mayar da martani cikin gaggawa a dukanin inda aka samu matsalar tsaro a birnin Abuja.

Da yake tsokaci akan yadda rundunar zata maida hankali akan tabbatar da tsaro a unguwanni, Egbetokun ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewar za’a samar da makamanciyar rundunar ta musamman da aka kaddamar a jihohin dake makwabtaka da Abuja domin magance matsalar tsaron.

Sace wani uba da ‘ya’yansa mata 6 a yankin Bwari na birnin Abuja a ranar 3 ga watan Janairun shekarar 2024 da muke ciki ya sabbaba bacin rai tsakanin ‘yan Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewar masu garkuwar sun hallaka daya daga cikin ‘yan matan mai suna Nabeebah sakamakon gazawar mahaifanta wajen biyan kudin fansar naira milyan 60.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG