Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Bayar Da Tabbacin Samar Da Tsaro a Zaben Gwamnoni

SUFETO JANAR MOHAMMED ADAMU ABUBAKAR

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ba da tabbacin samar da cikakken tsaro a duk sassan kasar don gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jahohi cikin kwanciyar hankali da lumana.

Sufeto janar na ‘yan sandan kasar Muhammad Abubakar Adamu ya jaddada hakan ne cikin wani sako da ya aikewa yan kasar dangane da da irin tsarin bayar da tsaro da sukayi, inda yake cewa wannan karo kam sun shirya tsaf don kare masu kada kuri'a.

Muhammad Adamu Abubakar, saboda haka yayi kira ga baki daya ‘yan Najeriya da su fito kwansu da kwarkwatarsu don kada kuri'unsu a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi, yana mai aikewa da sakon gargadin cewa duk wanda aka kama yana kokarin tada zaune tsaye yayin zaben, to hakika zai yabawa aya zakinta.

A cewar jagoran cibiyar raya demokradiyya a Najeriya Dakta Kole Shettima, ya ce koda yake a zaben shugaban kasa galibin jihohi anyi zaben lafiya amma yankuna irinsu Legas an sami tashe tashen hankali da yakamata ace an kaucewa, sai dai yan siyasa a Najeriya mutane ne da ka iya yin kome don ganin sunci zabe, inda yayi fatan zaben na gwamnoni da za ayi gobe za a sami tsaro fiye da wanda akai a baya.

kwararre kan tsarin demokaradiyya Farfesa jibrin Ibrahim, ya ce in an duba a Najeriya cikin shekara biyar din da suka gabata ba ranar da ba a samu tashin hankali ba, don haka ko a zaben na gwamnoni na goben in ansami tashin hankalin ba zai zama wani sabon abu ba, amma dai fatansu anan shine a daina tashin hankalin.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.