Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Imo Ta Saki Rochas Okorocha

Rochas Okorocha

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta saki tsohon gwamnan jihar Rochas Okorocha da aka kama bisa zargin shiga gidan da ke karkashin tsaron jami’an tsaro.

‘Yan sandan jihar Imo sun kama tsohon gwamnan Rochas Okorocha ne jiya Lahadi a gaban wani jerin gidajen da matarsa ta gina lokacin da yana gwamna, wanda gwamnati ta kwace bisa zargin cewa, matar ta gina gidajen ne da dukiyar talakawa.

A cikin hirarshi da Muryar Amurka, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Orlando Ikeokwu, ya ce an saki tsohon gwamnan ne jiya da yamma, bayan da aka dauke shi daga bakin gidan da rundunar ta ce yana neman tada hankali da lalata kaddarori zargin da tsohon gwamnan ya musanta.

Rochas Okorocha

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce an gayyaci tsohon gwamnan ne zuwa ofishin ‘yan sanda domin yi mashi tambayoyi dangane da gidajen da ke karkashin tsaron gwamnati, kuma idan bincike ya nuna ya aikata laifi za a tuhume shi.

SP Orlando Ikeokwu ya ce an tura jami’an ‘yan sanda a unguwar ne bayanda aka sami rahoton hargitsi a gidajen Royal Spring Palm, da ‘yan sanda suka isa wurin sai suka tarar tsohon gwamnan ya jagoranci wadansu mutane suka kutsa gidajen da gwamnati ta hana shiga.

Tsohon gwamnan wanda kuma yake wakiltar mazabar Imo ta Yamma a majalisar dattijai ya zargi gwamnan jihar Hope Uzodinma da umarta kama shi zargin da gwamnatin jihar ta musanta.

Kafin aukuwar wannan lamarin, wadansu ‘yan majalisar dokokin jihar Imo sun gabatar da bukatar kama tsohon gwamnan da kuma hukumta shi bayan ya yi ikirarin mallakar wata jami’a mai zaman kanta da ake kira Eastern Palm University (EPU) da suka ce an gida da kudin gwamnatin zamanin mulkin shi.

zaben-2019-mutanen-jihar-imo-sun-kalubalanci-zabin-gwamna-okorocha

an-bayyanar-da-sakamakon-zaben-dan-takarar-jihar-imo

dalilin-da-ya-sa-apc-ta-dakatar-da-okorocha-amosun

An shiga rikici da rudanin siyasa a jihar Imo tun lokacin zaben share fagen ‘yan takarar gwamna, da zaben wanda zai gaji Rochas Okorocha wanda da farko ya nemi dora surukinsa bisa karagar mulki, yunkurin da ya gamu da cikas. Tun a wancan lokacin ake kai ruwa rana tsakanin fitattun ‘yan siyasar jihar da tsohon gwamnan.