Wannan al'amari ya sa wasu daruruwan kungiyoyi masu zaman kansu yin harsashen gurfanar da hukumar EFCC a gaban kotu saboda kin bi masu haki tare da binciken mai gaskiya ko marar ita kamar yadda suka nema a shekarun baya.
Dakta Sani Abdullahi Wamban Shinkafi shi ne ya ke jagorantan kungiyoyin kuma ya ce sun aika da korafe korafe har so 16, akan binciken wasu jihohi irin su Zamfara da jihar Ekiti da ma wasu jihohi da Jamiyyar APC ke mulki amma EFCC ta yi buris da korafe korafen nasu. Akan haka ne yanzu suka hada takardunsu domin shigar da kara kotu.
To sai dai kwararre a fannin kundin tsarin mulkin kasa Barista Mainasara Ibrahim Umar ya ce kungiyoyin suna da hurumin kai kara amma fa sai sun hada da Ofishin Atoni Janar na kasa domin ita hukumar EFCC a karkashin Atoni Janar na kasa ta ke.
A bayan haka ma akwai wasu sharruda da kundin tsarin mulkin kasa ya tanada wadanda dole ne a bi su idan ana so a yi nasarar shigar da kara kotu.
A halin yanzu dai sufeto janar na rundunar 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya umarci duk wani dan sanda wanda ya ke makale a hukumar EFCC da ya koma ofishinsa na ainihi a wani mataki na tsaftace hukumar domin ta cigaba da aiki a bisa tafarkin Shugaba Muhammadu Buhari.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Facebook Forum