Wadanda rundunar ta kama dai sun hada da matasa da yara kanana masu shekaru kasa da 15, wanda kuma tuni ta tisa keyarsu zuwa kotu, yayin da kotun ta umurci a tsaresu a gidan gyara hali, don ci gaba da shara'a.
Khadimullah Zakariyya, mai shekaru 16, 'yan sandan sun zarge shi ne da daukar tutar kasar Rasha.
Wani yaro kuma mai shekaru 10 da 'yan sandan suka kama cikin wadanda ke satar dukiyar jama'a ya ce ya gano wani da ke raba wa yara kudi don su shiga zanga-zangar ne.
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Filato, DSP Alfred Alabo ya gargadi bata-gari da su guji aikata barna a jihar, domin hukuma ba za a kyalesu hakan nan ba.
Jami'in hulda da jama'a da gwamnan jihar Filato a Jos ta Arewan-Arewa, Nura Shehu ya ce sun yi mitin da masu ruwa da tsaki don tabbatar da zaman lafiya a garin na Jos.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto dai, dokar hana fita na aiki a garin Jos, daga karfe shida na yamma zuwa karfe goma sha biyu na rana.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5