Hedkwatar tsaron Najeriyar kazalika kuma tace babban hafsan hafsoshin tsaron kasar, Janaral Lucky Irabor ya umarci hedkwatocin rundunonin sojojin kasa, ruwa da na sama da su sallami jami'ansu dake da kasala ko rashin kazar kazar a bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.
Wata takardar umarnin hakan da Rear Admiral MB Nagenu ya sanyawa hanu a madadin babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriyar tace cikin wadanda za a kora daga aikin har da wadanda ake tababar biyayyarsu da zamansu a gidan soja bai da wani tasiri
Janaral Irabor ya nuna damuwa bisa dabi'u da munanan halayyar wasu mayakan kasar da son rai ya masu katutu.
A daidai lokacin da hedkatar tsaron ke bada wannan umarnin, tuni rundunar yaki da Boko haram a shiyyar arewa maso gabas wato Operation Hadin Kai OPHDK, ta yanke hukunci a kan wasu sojoji dari biyu da ashirin da takwas.
Ku Duba Wannan Ma Janar Faruk Yahaya Ya Bukaci Sojojin Najeriya Su Guji Tsoma Baki A SiyasaKotun sojin dai ta kori wasu jami'ai daga aki yayinda ta zartas da hukuncin dauri akan wasu sojoji talatin, wasu ashirin da biyar kuma ta rage masu girma wasu kuma ta hana a masu karin girma.
Duka wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun ke fuskantar kalubale a kusan duk sassan Najeriyar, baya ga yadda ake ganin yawan dakarun yayi karanci matuka, inda a kwanakin baya hedkwatar sojojin tace tana duba yiwuwar yin kiranye ga dakarun da sukai ritaya da su dawo su sa khaki don sake bada gudunmuwarsu ga kasar.