Rundunar Tsaron Farin Kaya Ta Yi Babban Kamu A Nasarawa

Jami'an Bada Kariya Ga Fararen Hula Na Civil Defense

Dubun wasu masu garkuwa da mutane da fashi da makami, ya cika, bayan hukumar tsaron a’lumma wato Civil Defence a jahar Nasarawa ta kara kaimi wajen zakulo bata gari dake cutar a’lummar jahar.

Batun yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ba wani sabon labara bane a sassa dabam-daban na Najeriya, amma a wannan karo dubun wasun su ya cika inda daya daga cikin su ya bayyana cewa bayan sun yi garkuwa da wani mutun aka biya kudin fansa, wasu mutane sun fanshi wanda aka yi garkuwa da shin ba tare da biyan su komai ba.

Wasu daga cikin wadanda aka kaman sun bayyana cewa bayan an biya kudin fansa kan wani da suka yi garkuwa dashi, wasu mutane daban sun tafi da yaron ba tare da sun basu ko sisin kwabo cikin kudin da suka karba ba.

Kwamandan rundunar "Civil Defence" a jahar Nasarawa, Muhammad Gidado Fari yace zasu ci gaba da farauta har sai sun tsabtace jahar Nasarawa daga hannun bata gari.

Kwamandan yace sun kama wani mai aikin welda dake tare da masu fashi da makamin wanda k eke balle karafen wurin ajiyan kudi. Rahotannin sun nuna da wannan mai welda ne aka balle wurin a jiyan kudi ma’aikatar filaye da wasu gidajen mai da sauran su.

Wakiliyarmu Zainab Babaji na dauke da Karin bayani a cikin wannan rahoto:

Your browser doesn’t support HTML5

AN KAMA MASU FASHI DA SATAR MUTANE A NASARAWA