Wannan ma ya biyo bayan kara wa’adin lokaci ne na biyan kudin bayan samun wani ragi a farashin kujerar da fiye da Naira dubu 50.
Shugaban hukumar alhazan Barista Abdullahi Mukhtar Muhammed, ya ce za a kammala amsar kudin don samarwa dukkan maniyyatan izinin tafiya “VISA” don gudanar da aikin hajjin.
Tun ranar Laraba 10 ga watan nan a ka kaddamar da fara jigilar alhazan daga jihar Katsina, inda wasu yankunan ma kamar Kaduna rukunin alhazan su ka sauka a Saudiyya.
Malamai na kan gaba a lamarin na aikin hajji don kula da nunawa maniyyatan dokokin aikin a aikace don gudun samun cikas.
Jami’in hukumar alhazan Umar Bala da tuni ya ke Madina ya shaidawa muryar Amurka yadda a ka tsara malaman za su kasance da alhazai a kowanne waje na sauke faralin.
Zuwa yanzu kimanin alhazai 5000 sun sauka a Saudiyya cikin kimanin alhazan Najeriya 65,000 da a ke sa ran za su gudanar da aikin hajjin na bana.
Domin Karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum