Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Tsaro Na Barazana Ga Hadin Kan Najeriya - Obasanjo


Olusegun Obasanjo
Olusegun Obasanjo

Wata budaddiyar wasika da tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya aikawa shugaba Muhammadu Buhari, ta nuna damuwa matuka kan yadda matsalar tsaro ke barazana ga Najeriya a matsayinta na kasa daya.

Wasikar wacce aka wallafa a jaridun Najeriya da dama a yau Litinin, ta yi bayani kan dumbin matsalolin da ke addabar kasar, amma ta fi mayar da hankali ne kan batun tsaro.

A wasikar, Obasanjo ya ce, duk da cewa ana ci gaba da fuskantar matsalar Boko Harm gwamnatin na ikirarin cewa tana samun nasara akansu.

Obasanjo ya ce ba wani nasara da ake samu musamman in an duba yadda har yanzu mayakan Boko Haram ke nuna karfin su, kuma suna ci gaba da ta da tarzoma a shiyyar arewa maso gabas, al'amarin da ke wofintar da ikirarin gwamnatin Buhari.

Cif Obasanjo ya kuma kara da cewa maganar da babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya ya yi inda ya ce, sojoji ba su da kwazo da himmar yin yaki, abin da ke jawo kalubale wajen cin galaba Boko Haram, wannan wata babbar shaida ce ta kasawar gwamnatin.

Matsalar rikicin manoma da makiyaya da abin ya faro kamar wasa da kuma
gwamnati ta yi maganar rikon sakainar kashi, sannu a hankali ta rikide zuwa aikaaikar 'yan bindiga, da garkuwa da mutane dan neman kudin fansa, ga kuma fashi da makami.

Abin bakin ciki ne inji Obasanjo yadda ake daukar Fulani makiyaya ne ke tafka wannan aikaaika. Sannan wasu 'yan Najeriya da abokan Najeriyar ke ganin cewa shugaba Buhari a matsayinsa na bafulatani, ya ce hakan abin bakin ciki ne.

Obasanjo ya kawo misali da kisan kare dangin da ya auku a kasar Rwanda, inda ya ce, barin kasar a hannun tsageru suna daukan doka a hannunsu, zai iya jefa Najeriya "cikin kangin kisan kare dangin da aka gani a Rwanda wanda ake tunanin ba zai faru ba sai kuma ga shi ya faru."

Daga dukkan alamu wasu kwararru a Najeriya irinsu Dr. Kabiru Adamu, sun amince da wasu daga cikin kalaman tsohon shugaban kasar. inda ya ce lallai
matsalar tsaro a Najeriya sai ta'azzara take a kusan duka sassan kasar
wanda a halin yanzu ma sai karuwa take yi fiye da a baya.

Shi ma tsohon gwamnan mulkin soja na jihohin Kano da Binuwai, Kanar
Aminu Isa Kontagora, ya ce Obasanjo a matsayinsa na dattijon kasa da ya
shugabanci kasar, dole ne a saurara masa, domin yana da hujjojin yin
wannan korafi.

A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG