Rundunar Tsaro Ta STF Ta Kwato Makamai Da Dama a Jihar Filato

Makamai da aka kwato

Rundunar ta ce ta kwato makaman ne a lokuta daban-daban yayin gudanar da aikinta na tabbatar da zaman lafiya.

Runduna ta musamman dake wanzar da tsaro a jihar Filato da sassan jihohin Bauchi da Kaduna, ta mika makamai 517 ga hukumar takaita yaduwar makamai a Najeriya.

Rundunar ta ce ta kwato makaman ne a lokuta daban-daban yayin gudanar da aikinta na tabbatar da zaman lafiya.

Makamai da aka kwato

Kwamandan rundunar ta Operation Safe Haven wanda shi ne Kwamandan runduna ta uku dake Jos, Manjo Janar Ibrahim Ali ya ce, rundunar za ta ci gaba da daukan matakan da suka dace wajen kakkabe bata-gari da kuma wayar da kan jama’a muhimmancin zaman lafiya.

Kodinetan Hukumar takaita yaduwar makamai a Najeriya, shiyyar Arewa ta Tsakiya, Manjo Janar Hamza Bature, mai murabus, ya yaba da kakarin dakarun ya kuma karfafa musu gwiwa kan su ci gaba da gudanar da aikinsu, har sai sun tsabtace al’umma daga mallakar makamai.

A watan Mayun shekarar 2021 ne gwamnatin tarayya ta kafa hukuma ta musamman da za ta rika tattara makamai da aka kwato daga hannun ‘yan ta’adda, ‘yan tawaye, barayi da sauransu, don adanasu a inda ya dace.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar STF Ta Kwato Dinbim Makamai