Da yake yi wa 'yan jaridu karin bayani kan aikace aikacen samar da tsaro a cikin kasar cikin wannan shekara mai karewa, daraktan sashin tattara bayanai kan irin arangamar da dakarun kasar ke yi Manjo janar Deward Buba yace an kwato makamannan ne daga watan janairun wannan shekara zuwa wannan wata na Disamba
Janaral Buba yace sojojin kasar sun yi gwagwagwa da 'yan ta'adda da
sauran barayin daji da ma masu aikata miyagun laifuka a sassan kasar
daban daban
Daraktan yace cikin bindigogin har da manya kirar AK 47 sama da dubu hudu, bindigogin da kuma aka kera su a gida sama dari bakwai, bindigogin toka sama da dari biyu
Wani babban abin da ke jan hankali dangane da yadda irin wadannan
dimbin makamai ke shigowa Najeriya wasu na ganin ba karamar matsala ba ce.
Amma Janaral Buba yace kowa yasan tarihin abin da ya faru a kasar
Libya da kuma dimbin dajin da ya zamanto ba kowa a cikinsa a yankin
Sahel da kuma aika aikar masu ikirarin jihadi na kasa da kasa a
yankin, wadannan na kadan daga cikin abinda yasa makamai ke tuttudowa cikin Najeriya.
Daraktan yace tsarin yanayin kan iyakokin Najeriya ma ya taimaka gaya
wajen shigo da makaman, musamman in aka yi la'akari da yadda aka cafke dimbin makaman a baya bayannan.
Sai dai kuma gwamnatin kasar ma a baya bayannan ta zargi jami'an tsaron kasar da saida wa 'yan ta'addan makamai, kamar yadda mai baiwa shugaban kasar shawarwari kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya bayyana.
Matsalar yaduwar makamai dai ta dade tana ciwa mahukuntan Najeriya tuwo a kwarya, dalilin ma kenan da yasa har aka kafa hukuma sukutum don yaki da yaduwar makamai a kasar.
Matakin da har yanzu aka kasa ganin tasirinsa a zahiri