Dakarun rundunar sun yi gwajin makamai a babban dajin barikin Soji dake garin Kontagora na jihar Naija.
Shugaban rundunar tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, wanda Manjo Janar Jal Jimoh ya wakilta, ya ce rundunar sojin sama na taimakawa rundunar sojin kasa don tabbatar da samun nasarar da ake bukata a yaki da ta’addanci.
Ya ci gaba da yin kira ga samun hadin kan ‘ya Najeriya wajen tsegunta bayanai da za su taimaka don kawar da bata gari da ke neman kawo rashin zaman lafiya a Najeriya.
Da ya ke jawabi shugaban rundunar sojin kasa ta Najeriya, Labtanal Janar Taoreed Lagbaja, wanda Manjo Janar SG Musa ya wakilta, ya ce horon da dakarunsu suka samu, ya hada da kwarewa ta musamman da za su iya tunkarar duk wani kalubale irin na rashin tsaro.
A daya bangaren kuma, masu sharhi kan lamuran tsaro irin su Dakta Yahuza Ahmed Getso, na nuna cewa duk da haka akwai bukatar rundunar ta kara samun hadin kan al’umma, kan yadda ake samun masu tseguntawa ‘yan bindiga da ke mayar da hannun agogo baya.
Domin Karin bayani saurari rahotan Mustpha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5