Manjo Janaral Olu Kolade kakakin rundunar sojojin Najeriya yace ya kamata 'yan jarida su maida hankali akan labaru dake nuna cigaba da aka samu, masu dadi tare da tantance kowane irin labari kafin su wallafi shi.
Ya kara da cewa bukata ce su ke yiwa 'yan jarida. Su mai da hankali akan labarai masu faranta rai da riba fiye da na asara kamar yadda suke yi yanzu.
Manjo Olu Kolade yayi jawabinsa ne a taron masu ruwa da tsaki da aka shirya tare da 'yan jarida domin neman hadin kai dangane da yadda aka yayata labaru na tashe tashen hankula a Najeriya.
Ana samun nasara akan yakin da kasar keyi da ta'adanci. Irin nasarorin da ake samu yakamata 'yan jarida su mayar da hankalinsu akai suna yayatawa. Ya kamata a mayar da hankali a kansu domin fadakar da jama'ar kasar da kuma duniya domin halin da ake jiki a zahiri.
Tsohon hafsan hasoshin Najeriya Janaral Martin Luther Agwai yayi karin haske a kan muradun da taron ke son cimma. Abun da suke son cimma shi ne yadda 'yan jarida zasu zauna su yi aikinsu yadda ya cancanta, su kuma jami'an tsaro yadda zasu yi nasu aikin da cancanta ba tare da zargin juna ba. Yakamata a samu fahimtar juna akan yadda zasu yi aiki domin jama'a su san abubuwan dake faruwa akan gaskiya da kuma yadda za'a samu zaman lafiya.
'Yan rjarida da jami'an tsaro su fadi abubuwan da suka kamata domin su samu fahimtar juna sosai, su san abubuwan dake faruwa. Akwai wasu abubuwan da jami'an tsaro na tsoron fadawa 'yan jarida suna tunanin kowa a duniya zai sani. Amma idan sun yadda da juna jami'an tsaro na iya fada masu su kuma su san yadda zasu yayatashi yadda ba zai kawo tashin hankali ba.
Tsohon shugaban kula da kafafan labaru na NBC Mr Tom Adaba ya fadi tasirin da yake gani taron zai yi tsakanin jami'an tsaro da 'yan jarida. Yace shin menene yasa bakin 'yan jarida da jami'an tsaro bai zo daya ba domin ci gaban kasar Najeriya. Yace idan 'yan jarida sun fadi wani abu sai sojoji su ce karya ne. Tunda lamarin ya zama haka shi yasa ya zama wajibi a yi taron domin a samu fahimtar juna. Yakamata a san damuwar sojoji da 'yan jarida da kuma damuwar 'yan jarida da sojoji. Idan an gane abun dake damun kowa za'a samu fahimta da cigaba.
Ga rahoton Saleh Ashaka.
Your browser doesn’t support HTML5