Rundunar Sojojin Najeriya Na Aikin Gyara Alakarta Da Al’umma

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kaddamar Da Aikin Ci Gaban Al'umma

Yayin da al’umma ke fama da matsalar rashin tsaro a Najeriya, rundunar sojin kasar ta ce ta na kara matsa kaimi wajen samar da tsaro ta fuskoki daban daban.

Babban hafsan mayakan kasa Lt. Gen. Faruk Yahaya ya ce bayan fita fagen da rundunar ke yi, haka ma tana na aiwatar da ayukan da ke kara hada kan sojoji da jama'a ta yadda za su samu damar taimakawa soji ga samar da tsaron kasa.

Bisa ga yadda rashin ke addabar Najeriya ta sassa daban daban, hukumomi da masanan tsaro na cewa lamarin samar da tsaro na bukatar gudunmuwa daga kowa.

Hakan baya rasa nasaba da yadda jami'an tsaro ke kokarin kusantar da kansu da jama'a ko da za su samu damar samun taimakon jama'ar kasa ga aikin nasu na samar da tsaro.

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kaddamar Da Aikin Ci Gaban Al'umma

Babban hafsan mayakan kasa Lt. Gen. Faruk Yahaya ya ce rundunar tana mayar da hankali wajen samarwa jama'a abubuwan more rayuwa da suke bukata, Kamar yadda ta yi a Jihohin Sakkwato da Imo inda ta gudanarda ayukka a bangarorin bunkasa ilimi da kiyon lafiya sai kuma samar da ruwa da wasu abubuwan inganta jin dadin Jama'a.

Ya ce yin hakan zai iya sa jama'a su fahimce cewa soji suna kaunar su ta yadda su kuma za su iya baiwa soji sahihan bayanai wadanda kan iya taimaka musu ga gudanar ayukan su cikin nasara.

To sai dai a lokacin da jami'an tsaron ke fafatukar samar da tsaro ta fuskoki daban daban su kuwa ‘yan ta'adda sun himmantu wajen kai hare-hare ga jama'a inda ko a ranar litinin ta wannan mako rundunar ‘yan sanda ta babbatar da wani hari da ‘yan ta'adda suka kai a wata kasuwa a Sabon Birni, inda a kokarin fatattakar ‘yan ta'adda jami'an tsaro uku da mutanen gari uku suka rasa rayukan.

Kakakin rundunar DSP Sanusi Abubakar, shine ya tabbatarwa jaridar Vanguard, amma bai amsa wayar wakilin sashen Hausa ba.

Dan majalisar jiha na yankin Aminu Almustapha Boza, ya ce ko da safiyar ranar Laraba, barayi sun tare hanya a garin Katsira sun kunnawa motar ‘yan kasuwa wuta kuma sun tafi da wasu mutane bayan harin da duka kai ranar litinin a kasuwar ‘Yar buluttu.

Duk wadannan hare-haren na faruwa ne lokacin da mayakan kasa na Najeriya ke taron bitar nasarorin da aka samu a wannan shekara da shirin sake daura damarar tinkarar kalubalen samar da tsaron kasa.

Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojojin Najeriya Na Aikin Gyara Alakarta Da Al’umma - 3'26"