Babban hafsan sojojin Nigeria ya mikawa gwamnatin Borno da Majalisar Dinkin Duniya wasu yara 184 da sojojin suka ceto daga hannun kungiyar Boko Haram.
Sojojin sun kama yaran ne suna dauke da makamai lokacin da suka gudanar da yaki da ‘yan Boko Haram din a jihar Borno. Yaran sun hada da mata da maza har ma da guragu.
Manjo Janar Rogers Nicholas wanda ya wakilci Janar Buratai ya ce babban hafsan su ya amince da sakin yaran 184 duk da cewa an samu wasun su rike da makamai, wasu kuma sun yi jigida da bama bamai.
Birgediya Abdulmalik Bulama Biu kwamandan rundunar shiya ta bakwai dake garin Maiduguri ya fadawa Sashen Hausa cewa yaran da suka mika su ga gwamnatin Borno kafin ita kuma ta mika su ga Majalisar Dinkin Duniya, yara ne da suka samu suna muamala da ‘yan ta’adda. Bisa dokar Majalisar Dinkin Duniya din duk wanda bai kai shekarun da za’a daukeshi babba ba, kimanin shekara 18, dole ne a sake shi da kyautata zaton za’a gyara halayensu su koma cikin jama’a.
Kwamishanan ma’aikara mata da walwalar matasa ta jihar Borno Binta Baba Shehu da ta wakilci gwamnan jihar ta fadawa yaran cewa Allah ya cece su daga cikin mugun aikin da bai kamata su shiga cik ba. Ta ce za su koya masu sana’oin da zasu dogara ga kai. Baicin hakan zasu yi kokari su maida su gun iyayensu. Wadanda kuma basu da iyaye zasu danka su ga hannun sarakunansu da shugabannin kananan hukumominsu.
Ibrahim Sisi, wakilin Majalisar Dinkin Duniya da ya karbi yaran daga hannun jihar Borno ya ce sakin yaran da sojojin Nigeria suka yi ba shi ne na farko ba. Kawo yanzu sojojin Nigeria sun mika masu kimanin yara dubu biyu kuma ya ce zasu yi duk iyakar kokarinsu su horas dasu su zama mutanen kwarai.
A saurari rahoton Haruna Dauda
Your browser doesn’t support HTML5