Rundunar sojin Najeriya ta yi bikin ban kwana da liyafar cin abincin dare biyo bayan ritayar wasu manyan jami'an ta 113 da suka yi ritaya bayan shafe shekaru talatin da biyar a aikin soji.
Manyan sojojin sun hada da babban Janar daya, da Laftanar Janar guda da masu mukamin Manjo Janar su sittin da bakwai, da kuma masu mukamin Birgediya Janar su arba'in da bakwai.
Babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron Najeriya Janar Leo Irabor, da tsohon babban hafsan hafsoshin mayakan Najeriya Laftanar Janar Farouk Yahaya da Darakta Janar na hukumar leken asiri na soji, Manjo Janar Samuerl Adebayo na daga cikin manyan sojojin da aka karrama a yayin bikin.
Da ya ke jawabi a wurin, Ministasn Tsaron Najeriya Muhammadu Badaru Abubakar ya yi jinnjinar ga sojojin bisa yadda suka sadaukar da rayuwar su ga aikin kare kasa.
Ministan ya tabbatarwa sojojin cewa, lallai za'a biya su hakkokin su ba tare da bata lokaci ba bisa la’akari da irin gagarumar gudunmuwar da su ka bayar a lokacin da suke bakin aiki.
Badaru Abubakar ya hori sojojin da su cigaba da marawa tsarin demokradiyya baya, ta yadda hakan zai sa Najeriya zama abin kwatance ga sauran kasashen da ke bin tafarkin dimokradiyya.
A na shi jawabin babban hafsan mayakan kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya ce wajibi ne sojojin da su ka yi ritayar da ga aikin, su gode wa Allah ganin sun yi ritaya cikin farin ciki da nasara.