Hafsan sajojin kasa na Najeriya Janar Tukur Burutai yace suna da karfin gwuiwar cewa zasu kawo karshen ta'adancin da Boko Haram ke yi cikin wa'adin da Shugaban kasa Muhammad Buhari ya diba masu.
Janar Burutai ya bayyana hakan ne lokacin da yake bude wani taron karawa juna sani na kwanaki uku tsakanin jami'an sojoji masu hulda da jama'a da kuma kafofin yada labarai a garin Maiduguri.
Janaran wanda kwamandan dake lura da arewa maso gabashin kasar Manjo Janar Yushau Abubakar ya wakilta yace rundunar sojin Najeriya da hadin kan sauran jami'an tsaro sun kai wani mataki mai mahimmanci a yakin da suke yi da 'yan ta'ada kuma zasu cigaba da yakarsu har sai sun gama dasu.
Shi ma daraktan hulda da jama'a Kanar Rabe Abubakar ya yiwa Muryar Amurka karin haske kan taronsu. Yace yanzu da hafsansu suna samun horo da kayan aiki saboda haka suna da karfafawa na cigaba da aikin. A matsayinsu na sojoji suna ba 'yan Najeriya tabbaci cewa suna iyakacin kokarinsu domin su kawo karshen ta'adancin.
Kanar Rabe ya roki jama'a da su kara masu karfin gwuiwa tare da basu bayyanan da zasu taimaka wurin zakulo 'yan ta'ada duk inda suke.
Dangane da karin kunar bakin wake dake wakana musamman a Borno da Adamawa yace lamarin nada nasaba da yakin sunkuru. Yace ko kasashen da suka cigaba bayan sun gama da 'yan ta'ada akan samu fashewar bamabamai nan da can na wani dan lokaci.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5