Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamu Ci Nasara a Kan Boko Haram- Buratai


Wasu Sojijin Najeriya a Bakin Aiki
Wasu Sojijin Najeriya a Bakin Aiki

Babban Hafsan sojin Najeriya, Manjo Janar Tukur Buratai ya jaddada cewa dakarun kasar za su cimma burinsa na dakile matsalar Boko Haram bisa lokacin da gwamnatin tarayya ta kayyade musu.

Buratai ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci sojojin runduna ta uku da ke Jos, a jahar Pilato ya na mai cewa rundanar ta kara azama wajen yakar kungiyar ta Boko Haram.

A cewarsa azamar da suka kara ne ya sa ‘ya’yan kungiyar suka kara zafafa hare-haren da suke kaiwa akan jama’a.

Tuni dai masu sharhi kan al’mauran yau da kullum suka fara tofa albarkacin bakinsu kan kalaman da Buratai ya yi, yayin wannan zaiyara ta sa.

“Son kowane dan Najeriya ne a cimma kawo karshen yakin, amma babban abu shi ne, sanin gaibu sai Allah, kuma babban abun da za a ce shi ne sojojin suna kokari, amma a ce wai rana kaza za a gama wannan yaki, zai zama abin mamaki da kuma bin tambaya.” In ji Dan Manjan.

A cewar Manjan, Boko Haram ba a Najeriya kawai su ke ba, akwai su a Kamaru da Chadi suna nan kuma a Nijar.

“ Saboda haka idan aka gama wannan yaki a Najeriya, za su iya bullowa daga wadannan kasashe da ke makwabtaka da Najeriya, sai dai mu yi musu addu’a Allah ya taimake su.” In ji Manjang.

Wakiliyar Muryar Amurka, Zainab Babaji, ta tambayeshi game da batun hare-haren bam da ake ci gaba da samu, sai ya ce jama’a na da rawar da za su taka.

“Yaki da ta’addanci ba na gwamnati ne kawai ba, kinga dai ba gwamnati ne ‘yan ta’addan nan ke kashewa ba, suna kashe jama’a ne, babu yadda za a ce baki za su shiga al’uma a ce ba a san da su ba, saboda haka gwamnati na da hakki, jama’a ma na da hakki.”

Domin jin cikakken bayani, saurari rahoton Zainab Babaji:

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG