Rundunar Sojin Najeriya Ta Tabbatar Da Mutuwar Dakarunta A Arewa Maso Gabashin Kasar

Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron, Manjo Janar Edward Buba

Shelkwatar tsaron kasar tace al’amarin ya faru ne yayin aikin kakkabe ‘yan ta’adda a wata babbar tungarsu da ake kira da Kusurwar Timbuktu.

Hukumomin sojan Najeriya sun tabbatar da mutuwar dakaru 22 yayin wani aikin wanzar da zaman lafiyar da suka kaddamar a yankin arewa maso gabashin kasar.

Shelkwatar tsaron kasar tace al’amarin ya faru ne yayin aikin kakkabe ‘yan ta’adda a wata babbar tungarsu da ake kira da Kusurwar Timbuktu.

“Gaba daya, yayin aikin, muna takaicin rasa dakarunmu 22 da suka mutu a bakin aiki da kuma dimbin wadanda suka jikkata a filin daga,” kamar yadda daraktan yada labaran shelkwatar tsaron Edward Buba ya bayyana a sanarwar daya fitar a jiya Lahadi.

A cewarsa, manufar samamen mai harsuna 3 da aka soma daga ranar 16 ga watan Janairun da muke ciki zuwa yau ita ce, tarwatsa tungar ‘yan ta’addar dake cikin kusurwar.

Sai dai a cewar Buba, dakarunsu sun yi nasarar hallaka fiye da ‘yan ta’adda 70 ciki harda kwamandojinsu a yayin samamen.

Shelkwatar tsaron ta kara da cewar, an samu nasara duk da amfani da abubuwa masu fashewar da ‘yan ta’addar suka yi domin dakile tunkarowar dakarun, kama daga wadanda aka daurawa ‘yan hari kunar bakin wake zuwa wadanda ake daurawa akan motoci.”

“Dakarun da suka lakanci dabarun ‘yan ta’addan sun dakile hare-harensu da dama, ciki harda harbo jirgi sama maras matuki da ‘yan ta’addar ke amfani,” a cewar shelkwatar tsaron.