A wani sabon farmaki da babban hafsan sojojin Najeriya Laftanal Kanal Tukur Yusuf Buratai ke jagoranta a Arewa maso gabashin kasar mai taken “Operation Kantana Jimlan” daga farkon wannan mako zuwa yanzu, sojojin sun kashe kimanin mayakan Boko Haram 134, tare da kone motocin yakin su guda 7. A wajajen yankin
“Operation Kantana Jimlan” wani bangare ne da rundunar sojin Najeriya ta kasa take gudanar da shi a karkashin “Operation Lafiya Dole wanda aka tsara shi domin kawo karshen ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP.
Jami’in sadawar a hedikwatar tsaron Najeriya, Navy kwamanda Abdulsalam Sani ya ce, rundunar sojin Najeriya ta sami nasarar kashe mayankan Boko Haram da ‘yan ta’addan ISWAP a yankin tafkin Chadi da garin Timbuktu.
Bugu da kari sojojin sun kuma cafke wasu da ke yiwa Boko Haram leken asiri su 16.
Masanin tsaro a Najeriya, Dr. Kabiru Adamu ya ce, irin wannan farmaki da rundunar sojin Najeriya ke kaiwa ‘yan ta’addan na da tasirin gaske, saboda wannan zai kawo karshen ‘yan ta’adda da ta’addanci gaba ki daya.
Mai sharhi kan sha'anin tsaro Wing Commander Musa Isa Salmanu ya ce, ya kamata a nemi ko a kaddamar da bincike kan menene ya sa wasu matasa ke mika kansu ga Boko Haram a matsyin mayaka.
A makon da ya gabata, hedkwatar dakarun kawancen kasashen yankin Tafkin Chadi ta fidda sanarwa, inda tace ta gano wani shirin karkashin kasa da Boko Haram ke yi na diban sabbin mayaka.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5