Shugabannin kasashen duniya ‘yan ba ruwanmu, sun yi wani babban taro ta yanar gozo inda suka yi nazari tare da tattauna hanyoyin da za su hada karfi da karfe don su yaki cutar coronavirus wadda ta bazu a duniya kuma ta ke ci gaba da kisa.
Shugabannin kungiyoyi, sun yi amfani da wannan hanyar ta zamani don gudanar da cikakken taro mai tasirin gaske don daukar matakan da za su kawo sauki tsakanin kasashen duniya ‘yan ba-ruwanmu, game da hanyoyin da za su bi don tallafa wa juna ta bangaren tattalin arziki tare da hadin gwiwar kasa da kasa.
Taron ya hada har da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashen duniya masu arziki don tsara hanyoyin da za a bi a taimaka wa kasashen masu tasowa ta wannan kungiyar don su yaki bazuwar cutar coronavirus.
Daya daga cikin masu sharhi akan al’amuran tattalin arziki a Najeriya Malam Ahmed Yusuf, ya ce kafa kungiyar ya yi daidai saboda yaki da cutar coronavirus ba zai yi wu ba in babu karfin tattalin arziki da kuma tallafa wa kasashe don yaki da bazuwar cutar ta hanyar ba da tallafi ga wadanda ba sa iya ciyar da kansu.
Malam Abubakar Abdullahi Gwandu, shi ma masanin harkokin tattalin arziki ne, ya kuma ce taron na da muhimmanci duba da cewa annobar coronavirus wani kalubale ne ga duniya baki daya.
Ya kara da cewa, kasa daya ba za ta iya maganin annobar ita kadai ba, saboda haka dole ne a hada hannu don a ci gajiyar abubuwa da dama, musamman yadda za a dakile yaduwarta daga wata kasa zuwa wata kasa.
Saurari karin bayani daga Umar Faruk Musa.
Facebook Forum