A Najeriya, hukumomin sun fara sassauta tsauraran matakan hana yaduwar cutar corona daga jiya Litini a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, da Lagos, birni mafi girma a kasar.
Hakan na nufin an sake bude hada-hadar tattalin arziki a kasar da ta fi karfin tattalin arziki a Afirka, bayan makonni sama da hudu da tsayar da harkoki.
A kasar Tanzania kuma, Shugaba John Magufuli ya yi watsi da gwajin cutar corona da ake yi a kasar da cewa bai da inganci, bayan da gwajin ya nuna har dabbobi da ‘ya’yan itatuwa ma sun kamu da cutar, ciki har da akuya da gwanda.
A Kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo kuwa, tashin gwauron zabi da farashi kayan abinci ya yi, ya sa har jami’an Majalisar Dinkin Duniya da jami’an gwamnati, na bayyana al’amarin da wani yunkuri na neman kazamar riba, a lokacin da duniya ke fama da matsala.
Facebook Forum