Daraktan yada labarai na rundunar sojojin Najeriya ya bayyanawa wakilin sashen Hausa na muryar Amurka cewa a jiya ne rundunar sojojin Najeriya ta sami kiran kai daukin gaggawa daga hukumar bada rahoton bada daukin gaggawa ta ruwa ta duniya, cewa ‘yan fashin teku sun kai farmaki kan wani katafaren jirgin ruwa mai dauke da tutar kasar burtaniya daya tashi daga Najeriya zuwa kasar Congo.
Kwamandan ya kara da cewa take tanke suka tura jirgin ruwan yaki domin kaiwa jirgin ruwan dauki, kuma mayakan sojin ruwan Najeriyar sun yi musayar wuta da manyan makamai inda daga karshe ‘yan fashin suka ranta a nakare, kana sojojin suka ceto jirgin da ma’aikatan sa.
Jami’in ya bayyana cewa yanzu haka jirgin yana hannun sojojin ruwan na Najeriya kuma da zarar sun kammala bincike zasu bar shi ya kama hanya zuwa inda ya dosa.
Daga karshe kwamandan ya bayyana cewa wannan na daya daga cikin ayyukan sintiri da suke yi wanda suke wa take da operation tsare teku, kamar yadda babban hafsan mayakan ruwan Najeriya ya dauki aniyar gamawa da ‘yan fashin teku.
Comrade Abubakar Abdussalam, kwararre ne akan harkokin sufurin ruwa kuma tsohon jami’ain hukumar jiragen ruwan Najeriya ya ce kamar yadda ake da ‘yan fashi akan titunan motoci haka suke a ruwa musamman idan aka sami akasi jirgi ya iso wurin da zai sauke kaya amma ya taradda wasu jiragen basu kammala ba, sai a basu umurnin dakatawa a cikin teku ta haka ne ‘yan fashin suke kai masu hari.
Hassan Maina Kaina.