Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Oyo Ta Kafa Hukumar Dakile Ambaliyar Ruwa


Irin illar da ambaliyan ruwa ka iya haddasawa
Irin illar da ambaliyan ruwa ka iya haddasawa

Sakamakon gargadin da hukumar bada taimakon gaggawa wato NEMA ta bayar makon jiya game da ambaliyan ruwa awasu jihohin kasar da suka hada da jihar Oyo, gwamnatin jihar ta kafa wata hukuma akan muhalli da kotu na musamman domin hukumta masu kin bin dokokin muhalli da zummar kacewa ambaliyan ruwa a jihar

Hukumar da gwamnatin ta kafa ta kumshi ma'aikatu guda ukku ko hudu da suka hada da ma'aikatar muhalli da ma'aikatar filaye da ma'aikatar ayyuka da jami'an 'yansanda da dogarawan tsaron farar hula ko Civil Defence.

Chief Ishola Adisa kwamishanan muhalli na jihar yace aikin wannan hukumar shi ne ta kama duk wanda ya karya dokokin muhalli a jihar. An kuma kafa kotun muhalli na mausamman da zai saurari kararraki dake da alaka da karya dokokin muhalli a kuma hukumtashi nan take.

Gwamnatin ta dauki matakan ne domin ilimantar da al'ummarta domin su kaucewa cunkushewa hanyoyin ruwa domin hana aukuwar ambaliyan ruwa a duk fadin jihar.

A shekarar 2011 aka yi wata munmunar ambaliyar ruwa a jihar da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama., da lalata gidaje da makarantu da asibitoci da hanyoyi da gadoji da dai sauransu.

Illar ambaliyan ruwa
Illar ambaliyan ruwa

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:53 0:00

XS
SM
MD
LG