Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cogen Kasafin Kudi Ya Haifi Kungiyar Adalci A Majalisar Wakilai- Musa Soba


Yakubu Dogara, kakakin majalisar wakilan Najeriya
Yakubu Dogara, kakakin majalisar wakilan Najeriya

Onarebul Muhammad Musa Soba na jam'iyyar APC dake wakiltar mazabar Soba ta jihar Kaduna wanda kuma shi ne kakain kungiyar adalci ko Transparency Group a majalisar wakilan Najeriya ya bayyana manufofin kungiyar

Sun kafa kungiyar ne a lokacin da , wai suka fahimci cewa akwai wasu abubuwa da ake yi ba daidai ba.

Musa Soba yace akwai abubuwa na kumbiya kumbiya wadanda suka so dole ne a fallasa, a falle kowa ya san cewa ga yadda ake yin abun.

Kasancewa majalisa ce take da ikon yin dokoki bai kamata a ce wasu 'yan tsiraru ne zasu dinga karkata alamura sai abun da suka so. Kungiyar bata fito fili ba sai lokacin da aka aiwatar da kasafin kudi da ya nuna masu cewa ba abun da suka amince dashi ba aka mikawa shugaban kasa.

Basu yadda da cogen da aka yiwa kasafin kudin shekarar 2016 saboda an zalunci 'yan Najeriya.

Yace majalisa ta kunshi mutane 360. Goma ne shugabannin majalisar kana akwai shugabannin kwamitoci 46. Wadannan tsiararun su 56 suke dorawa majalisa nasu muradun kuma basu da ikon yin hakan. Su ne suke canza abun da majalisar ta amince dashi su gabatar da wani abu daban. Dalili ke nan suka ce basu yadda ba, sai an yi fallasa.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:21 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG