Rundunar Sojin Mayakan Sama dake Maiduguri Tana Binciken Kisan da Wani Jam'inta Yayi

Kwamandan rundunra mayakan Charles Ohole yayinda yake yiwa manema labarai bayani

Rundunar sojojin mayakan saman Najeriya tana binciken yadda wani jami'inta ya kashe Malam Ibrahim Bulama dan shekara sittin da haihuwa a birnin Maiduguri.

Kwamandan mayakan Charles Ohole shi ya bayyanawa manema labarai binciken da suke yi akan lamarin a birnin Maiduguri tare da matakin da suka dauka kawo yanzu a kan kisan.

Yace ranar bakwai ga wannan watan ne wani jami'insu mai suna Kamar Usman ya tashi aiki da misalin karfe goma na dare a kan hanyarsa ta komawa wajen kwanansa. Da wasu mutane suka ganshi sai suka ruga da gudu shi kuma sai ya isa wurin ya ga dalilin da ya sasu gudu.

Jami'in ya shiga leka dakuna a wani gida a anuguwar da ake kira Okona. Daki na karshe da ya leka ya ga wata mace da wani mutum a dakin kafin ya ankara an kai masa hari ta baya. Shi mutumin da ya gani da mace ya kwace bindigarsa. Ya ji ciwo saboda harin da aka kai masa sai ya fice ya samu abokan aikinsa wadanda suka kawo mashi taimako.

Sojojin da ya kawo domin su taimaka masa su kuma kwato bindigarsa suka lakadawa Ibrahim Bulama dan karen kashi har ya rasa ransa.

Kwamandan yace bayanan da suke dasu ke nan amma bayan sun kammala cikakken bincike zasu sanar da duniya gaskiyar lamarin.

To saidai rahotanni dake fitowa daga cikin gari na cewa batun na fyade ne. Amma kwamandan yace basu tabbatar da wannan batun ba. Suna cigaba da bincike har sai sun kammala.

Kwamandan yace ko menene ma kuma kowanene yake da hannu ciki, walau soja ko farar hula, za'a yi adalci.

Kamar Usman sojan da ya sha duka a hannun Ibrahim Bulama yana asibiti amma shi kuma sojan da ya lakadawa Ibrahim Bulama kashi yana kulle.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojin Mayakan Sama dake Maiduguri Tana Binciken Kisa da Wani Jam'inta Yayi - 3' 35"