Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar tallafin kayan abinci na gwamnatin tarayya daga hannun hukumar kwastan din kasar.
Inji gwamnan 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kone azuzuwan karatu na makarantun firamare 5335. Sun kone ko sun lalata makarantun firamare 510. Sun yi rugurugu da makarantun sakandare 38 da na gaba da sakandare biyu. Sun lalata ko wasu gine-gine 601 banda hanyoyi da asibitoci da wutar lantarki da sauran ababen more rayuwa da suka lalata.
Gwamnan yace saboda haka sun yi maraba da duk taimakon da za'a kawo masu. Yace zasu bi duk hanyoyin da suka dace na raba kayan abincin da aka basu. Ya kara da mika kokon barar neman kayan gine-gine domin su cigaba da sake gina wuraren da aka lalata.