Wannan atisaye da ya kunshi kasashen duniya 30 da rundunar sojojin ruwan Najeriya ke jagoranta mai taken Operation Obangeme, za a shafe makonni biyu anayi a mashigar tekun Guinea. Wakilin Muryar Amurka, Hassan Maina Kaina, ya tambayi daraktan watsa labarai na hedikwatar sojojin ruwan Najeriya, kwamanda Christian Ezekobe, ko menene tasiri da makasudin wannan atisaye?
A cewar kakakin wannan atisaye zai kara inganta aiki da hadin kai tsakanin sojojin ruwa dake wannan shiya, zai kuma taimaka wajen inganta jajircewar sojon ruwan wajen yakar ‘yan fashin teku ba wai kadai a ruwan dake cikin Najeriya ba, har da ilahirin mashigar tekun Guinea a yankin kasashen dake yankin Afirka ta yamma.
Ganin wannan shine babban atisayen mayakan ruwa na kasa da kasa irinsa na farko da aka taba shiryawa, ya kuma kunshi dakarun ruwa na wasu manyan kasashen duniya irin su Amurka da Faransa da Jamus.
A karshen wannan atisaye zai bada damar inganta aikace aikacen mayakan ruwa dake kasashen yammacin Afirka, dana kasashen dake tsakiyar Afirka, kasancewar mashigar tekun Guinea ya faro ne daga kasar Senegal ya isa har kasar Angola. Don haka yana da kyau duk sojojin dake wannan shiya su hada kai tsakanin su.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5