Rundunar Soja dake Maiduguri Ta Takaita Zirga-zirgan Ababen Hawa Lokacin Bikin Kirsimati Sabili da Dalilan Tsaro

Wasu manyan jami'an sojojin Najeriya

Rundunar sojan Najeriya ta bakwai dake Maiduguri ta sanar da samun wasu rahotanni dake cewa wasu na shirin kai hare-hare lokacin bukukuwan kirsimati da sabuwar shekara.

Sabili da rahotannin da tace ta samu rundunar ta hana zirga-zirgan ababen hawa tun daga karfe shidan marece na ranar Laraba, wato yau, har zuwa karfe bakwai na safiyar Lahadi.

Sanarwar dake dauke da sa hannun mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar sojan Najeriya shiya ta bakwai dake Maiduguri, Kanal Sani Usman tace haramcin bai shafi kafofin yada labarai ba da ma'aikatan asibiti da kuma ma'aikatan kwana-kwana.

Kanal Usman ya kira al'ummar jihar da su zama masu bin doka da oda. Yace rundunarsu a shirye take ta tabbatar da cewa ta maido da zaman lafiya a jihar ta kuma kawo karshen hare-haren da 'yan Boko Haram ke kaiwa. Ya kira jama'a da su dinga sa hankali akan yadda alamura ke tafiya a inda suke.

Wasu al'ummar jihar sun ce su suna ganin ba'a yi masu adalci ba. Suka ce ga wuraren da 'yan Boko Haram suka mamaye maimakon sojojin su kwatosu sai kuma sun kutuntamasu. Sun ce su dake cikin garin Maiduguri suna iyakar kare garin da tabbatar da zaman lafiya. 'Yan kato da gora ma suma basa barci duk a kokarin tabbatar da tsaron Maiduguri. Sabili da haka bai kamata sojoji su dannesu ba. Suka ce da zara wani dan biki ya zo sai su hana mutane sakat, su hana fita. Sai su rufe mutane cikin gidajensu.

Amma wasu suna ganin dacewar matakan idan har za'a samu lafiya kuma ba za'a kawo hari ba a garin lokacin bikin kirsimatin. Suna fata matakan su zama masu alheri. Sun kira jama'a su yi kokari su bi doka.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Soja dake Maiduguri Ta Takaita Zirga-zirgan Ababen Hawa Lokcin Bikin Kirsimati Sabili da Dalilan Tsaro - 3' 18"