Rundunar Mayakan Ruwa Na Taka Rawa Don Samar Da Zaman Lafiya a Najeriya - Vice Admiral Gambo

Shugaban sashen Hausa Aliyu mustapha, da babban hafsan hafsoshin mayakan ruwan Najeriya Vice Admiral Auwal Zubairu Gambo

Yayin da lamarin tsaro ke ci gaba da ta’azzara a wasu sassan Najeriya, rundunar mayakan ruwa na taka muhimmiyar rawa wajen ganin an samar da zaman lafiya a ciki da wajen kasa.

Rundunar sojojin ruwan Najeriya, wacce kundin tsarin mulkin kasa ya samar da zummar kare yanci da diyaucin kasar, ba kasafai ake jin duriyarta ba, kamar sauran takwarorinta na rundunar mayakan kasa da ta sama, saboda ita aka daurawa alhakin kare Najeriya ta ruwa, a cewar Vice Admiral Auwal Zubairu Gambo.

Cikin tattaunawa da shugaban sashen Hausa Aliyu mustapha, babban hafsan hafsoshin mayakan ruwan Najeriya Vice Admiral Auwal Zubairu Gambo, ya ce sojojin ruwa suna aikin hada hadin gwiwa sauran rundunonin tsaro don tabbatar a aikin samar da zaman lafiya a kasar.

Haka kuma babban hafsan mayakan ruwan, ya shaidawa sashen Hausa cewa rundunar ta na da wasu zaratan sojoji na musamman da ke iya fafatawa ta ruwa ko ta sama ko kasa.

Wadannan sojoji na musamman suna gudanar da ayyuka masu sarkakiya ko wahala irin na takwarorinsu na kasar Amurka da ake kira Seal ko Special Boat Service na Burtaniya, aikin da suke yi sun banbanta domin akan horar da su kan duk wani abu da ka iya tasowa ko na gaggawa domin samar da tsaron kasa.

Shugaban sashen Hausa Aliyu mustapha, da babban hafsan hafsoshin mayakan ruwan Najeriya Vice Admiral Auwal Zubairu Gambo

Vice Admiral Gambo, ya ce duk da kasancewarsu sojojin ruwa, aikinsu bai fara kuma ya kare a cikin ruwa ba, domin a halin yanzu a kwai sojoji kimanin dubu daya da ke aiki kafada da kafada da sojojin kasa a kan tudu.

Haka kuma yanzu haka a kwai dakarun ruwa dake can suna kuma aikin tunkarar yan ta'addar Boko Haram a yankin Tafkin Tchadi, a cewar Admiral Auwal, musamman cikin ruwan tafkin ganin wannan fanni shine bangarensu da suka fi kwarewa.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Rawar Da Rundunar Mayakan Ruwa Ke Takawa Don Samar Da Tsaron Najeriya - 2'49"