Kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’ah wa Ikamatis Sunna a Najeriya JIBWIS, ta yi kira ga mahukuntan kasar da su “gaggauta” yin hukunci ga wasu sojojin kasar biyu da ake zargi da kisan Sheikh Goni Gasua Aisami.
Rundunar ‘yan sanda jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta sanar da kama wasu sojoji biyu, wadanda ake tuhuma da kashe Aisami a ranar Juma’ar da ta gabata.
Shugaban kungiyar ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya yi kira ga mahukuntan kamar yadda wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Litinin ta nuna.
Aisami na hanyarsa ta komawa garin Gashua daga Kano ne a lokacin da lamarin ya faru, inda wani soja ya nemi ya rage masa hanya, daga bisani kuma sojan ya bindige malamin har lahira ya kuma yi yunkurin guduwa da motarsa.
“Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukan mataki akan wasu sojojin Najeriya guda biyu da suka kashe daya daga cikin malaman kungiyar Sheikh Gwani Aisami da ke garin Gashua ta jihar Yobe.
"Muna yaba wa hukumar 'yan sanda da suka dauki mataki nan take na cafke sojojin da aka samu a daji wajen gawar marigayin.” In ji Sheikh Bala Lau.
Sheikh Bala Lau ya kuma ce babu shakka kungiyar ba za ta amince akan wannan “ta'addanci ba,” yana mai cewa “sun zura ido da kunnuwa domin sauraren yadda za ta kaya wajen aiwatar musu da hukunci cikin gaggawa.”
Kakakin rundunar 'yan sanda a Yobe, Dungus Abdulkarim, wanda ya tabbatar da kama sojojin, ya kuma ce bayan kammala bincike zai yi karin bayani kan wannan al’amari.
Jaridar Premium Times ta bayyana cewa Abdulkareem ya ce sojojin sun amsa laifin kashe shehin malamin.