Kwamandodjin rundunar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika a Somalia ta AMISOM, sun fada a jiya Asabar cewa sun amince da kaddamar da wasu sabbin ayyuka da zasu auna mayakan al-Shabab a Somalia.
WASHINGTON DC —
A cewar rundunar ta AMISOM, sabbin ayyukan sojin, za a gudanar da su ne a huskoki uku a wani yunkurin kakkabe kungiyar ‘yan ta’addan daga mabuyar su a yankin.
Da yake jawabi a karshen wani taron kwanaki biyar na kwamnadodjin sojojin a Mogadishu, mukaddashin wakili na musmman ga shugaban hukumar zartarwar kugniayr AU a Somalia, Simon Mulongo ya yi bayani dalla dalla a kan yadda za a gudanar da ayyukan.
Yace ayyukan sun hada da taimakawa tsarin mika mulki a Somalia da kuma ayyukan tabbatar da zaman lafiya, inda za a kai samame a mabuyar mayakan al-Shaba da kuma inganta tsaro a cibiyoyin al’umma, inji Mulongo.