Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta babban birnin tarayyar Najeriya (FEMA), ta tabbatar da cewa ba’a samu asarar rai ba a rugujewar ginin data afku cikin dare a yankin Garki na birnin Abuja.
A cewar mai rikon mukamin Babbar Daraktar Hukumar ta FEMA, ana gudanar da gyare-gyare ne akan ginin wanda ya kasance bene mai hawa 4.
Shaidun gani da ido sun shaidawa tashar talabijin ta Channels cewa, galibin masu aikin ginin sun tashi daga aiki, sa’ilin da benen ya ruguje.
Jami’an hukumar bada agajin gaggawan sun dora alhakin faruwar lamarin akan dan kwangilar, saboda bijirewa umarnin da hukumar kula da gine-gine ta birnin Abuja ta bashi na ya dakatar da aiki.
A cewar FEMA, tuni aka samu nasarar kubutar da mutane 3 da suka samu kananan raunuka daga wurin.