Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rugujewar Gini Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Uku Da Raunata Da Dama A Kano


Rugujewar Gini
Rugujewar Gini

Rahotanni daga kaffafen yada labaran cikin gida na cewa akalla mutane 11 ne aka samo a karkashin baraguzan ginin da ake kan ginawa. 

ABUJA, NAJERIYA - Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu sannan ma'aikata da dama suka jikkata yayin da wani gini ya ribza da su a jihar Kano a yau Juma'a, 26 ga Afrilu, 2024.

Wasu ma’aikata da ba a tantance adadinsu ba sun makale a lokacin da gini ya rufta a unguwar Kuntau da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

Jami’an bayar da agajin gaggawa na hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) da hukumar kashe gobara ta jihar sun yi ta aikin ceto wadanda suka makale.

An samu nasarar ceto mutane biyu kuma an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.

An dai ci gaba da aikin tono, inda masu ba da agajin suka yi ta kokarin ganowa da ceto duk wani da ya rage a makale.

Kawo yanzu dai an gano wasu gawarwaki daga wurin, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da adadinsu ba.

Har yanzu dai ba a san musabbabin rugujewar ginin ba, kuma hukumomin yankin na gudanar da bincike kan lamarin.

Ana sa ran ƙarin cikakkun bayanai game da afkuwan lamarin.

~Yusuf Aminu Yusuf ~

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG