Duk da cewa masana na ganin wannan mataki na kan gaba la’akari da matsalalolin tsaro dake kara ta’azzara a kasar, Kasancewar a makon nan ne dai wasu yan’ ta’adda suka kai hari a gidan gyara hali dake Kuje wanda kasurguman fursunoni da dama ciki har da yan’boko haram suka arce.
Duk da cewa sanya wannan doka na a rufe wuraren shakatawa dake babbar birnin na Abuja ba sabo bane, amma kwararru na ganin matakin ya zo akan lokaci da ake bukata.
Wannan mataki dai ya janyo kace-nace tsakanin jama’a musamman masu gudanar da harkokin kasuwancinsu da ma mutane da kan ziyarci ire iren wuraren shakatawa don samun nishadi da hutu, wasu na ganin an take musu hakkinsu da walwalansu sai dai kwararre a harkar raya birane (Town Planner) Zayyanu Muhammad, ya ce kamata ya yi mutane su fahimci tsarin da aka gina birnin da shi a kuma mutunta doka.
Masanin tsaro a Najeriya Kabiru Adamu, na da ra’ayin cewar wannan mataki ba zai haifar da da mai ido ba har sai an dakile hanyoyin da ke sa masu aikata laifi gudanar da laifukansu domin idan an rufe wata hanya za a bude wata.
Tun farko an saka wannan doka ne saboda tsaro bayan wasu bata gari sun kai farmaki wani wajen shakatawa a birnin.
A iya cewa bikin babbar sallah na bana ya zo wa al’ummar birnin Abuja cikin yanayi na rashin armashi da fargaba tabarbarewar tsaro. Fata dai shine samun saukin gudanar da rayuwa ta yau da kullum.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5