WASHINGTON, DC —
Lamarin nan na rufe iyakar Najeriya da sauran makwabtan kasashe, ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin jama'a dake zauren a cikin Najeriya da kuma sauran kasashen, inda wasu ke nuna yadda rufe iyakar ta kawo matsaloli da yawa, wasu kuwa cewa suke wannan mataki ya taimaka wajen hana shigo da kayan ta'addanci, kwayoyi, da dai sauran su.
Shakka babu wannan lamari na rufe iyakar Najeriya ya kawo damuwa da matsaloli iri iri ga direbobi, da 'yan kasuwa, har ma da matafiya.
Wakilin Muryar Amurka Ridwan Abbas, ya samu jin tabakin jama'a daga babban birnin Accra dake kasar Ghana, kan yadda wannan mataki na rufe iyakar Najeriya ya shafe su, da rayuwarsu.
Ga saurari sautin rahoto daga wakilin Muryar Amurka Ridwan Abbas.
Your browser doesn’t support HTML5