Rufe Bodar Najeriya Da Benin, Yankin Babanna Na Cikin Tsaka Mai Wuya

Ayarin motoci na tsallaka kan iyaka daga kasar Libiya

Rashin bude Bodar Nigeria da kasar Janhuriyar Benin dake yankin Babanna a jihar Neja na ci gaba da jefa al'ummomin yankin cikin yanayi na damuwa sakamakon yadda harkokin kasuwanci su ka samu koma baya a tsakanin kasashen biyu

Tun a lokacin tsohuwar gwamnatin Shugaba Buhari ne dai aka rufe wannan boda sakamakon matakin da gwamnatin Buharin ta dauka na rufe iyakokin kasar ta kasa a wancan lokaci,

Iyakar ta Babanna dake karamar hukumar Borgu a jihar Neja tana da Babbar Kasuwar kasa da kasa da ta hada kasashen Nigeria da Beni da kuma kasar Jamhuriyar Nijar harma da wasu kasashen Africa ta yamma,

A yanzu dai gwamnatin jihar ta kafa wata hukuma ta musamman da ta ke kira "Babanna Boda Deployment Agency" da nufin bunkasa tattalin arzikin mazauna wannan yanki,

A wani taron masu ruwa da tsaki akan lamarin kasuwar kasa da kasa ta Babannan, mahalarta taron sun tattauna abubuwa guda uku da suka hada da bukatar gwamnatin Nigeria ta sake bude wannan bode da kuma kara inganta hanyoyin zirga zirga da kuma tabbatar da ingantuwar tsaro.

A hirar shi da Muryar Amurka, Shugaban karamar hukumar Borgu Hon.Suleman Yarima kilishi ya bayyana cewa, dama suna da alaka mai karfi a tsakanin yankin Faraku ta kasar Benin da kuma Borgu ta Nigeria saboda haka yace bude wannan boda zai taimaka wajan kara karfin wannan dangantaka.

Suma dai Sarakuna iyayen kasa sun jaddada bukatar ganin hukumomi sun waiwayi yankin na Babanna ko baya ga bude Bude Bodarma lamarin rashin tsaro na zama wata babbar barazana.

Tunda farko Wani jami,in hukumar Kwastan a Nigeria Ma'aruf Aliyu Goro da ya halarci wannan taro yace idan aka shawo kan matsalolin da yasa aka rufe Bodar a baya, za a bude ta nan bada jimawa ba.

Bayanai dai na nuna wannan yanki na Babanna yayi matukar komawa baya ta fuskar ci gaban tattalin arziki sakamakon rufe wannan iyaka na kusan shekaru shidda zuwa Bakwai.

Saurari cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Rufe Bodar Najeriya Da Benin, Yankin Babanna Na Cikin Tsaka Mai Wuya