Daga dukan alamu rufe iyakokin kasa da Hukumar Hana Fasakwabri ta Najeriya ta yi ya haifar da alheri, domin kuwa mai magana da yawun hukumar mukaddashin Shugaban Kwastan Joseph Attah, ya ce an samu Naira Triliyan 1.3 a maimakon Naira biliyan 937 da Gwamnati ta ba hukumar izinin samowa.
Masana da masu fashin baki na ganin dole ne mahukunta su sa ido kan yadda ake gudanar da harkokin kudi da ake samu a kasar baki daya, idan ana son a samu cigaba mai dorewa kamar yadda tsohon mukaddashin Shugaban Kungiyar kwadago ta kasa Komred Isa Tijjani ya yi bayani.
Ya ce ai wanan ikirari da hukumar ta yi wai ta samo karin kudaden shiga, yaudara ce kawai ta ke yi wa 'yan kasa, saboda ko an rufe boda ko an bude boda ba zai hana a yi fasakwabri ba, kuma a ganin sa ana hada kai ne da ma'aikatan hukumar hana fasakwabri ne, saboda haka ba abin da za a fasa.
To saida ga mai fashin baki a al'amuran yau da kullum Mohammed Ishaq Usman, yana ganin Hukumar Hana Fasakwabri ta yi rawar gani domin ai wannan yunkuri na rufe boda hanya ce da aka yi domin a samu karin kudaden shiga, kuma an samu, sai dai yana gani dole ayi sara a dubi bakin gatari saboda akwai yarjejeniyoyi da ake da shi na kasuwanci da Kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.
Amma ga Shugaban Kungiyar mai sa ido a harkokin gudanar da mulki Auwal Musa Rafsanjani ya ce kamata ya yi a samu shugabannin da suka san abinda suke yi, saboda su sarrafa kudaden ta hanyar da zai kyautata wa al'umman kasa, ba wai a bar wa wasu 'yan kalilan masu sace kudaden ba,.
Yana mai fatan a rika tantance wadanda za a rika dauka aiki mussaman aikin da ya shafi mu'amala da kudi domin a tabbatar cewa kwararru masu gaskiya ne da rikon amana.
Har yanzu iyakokin kasar a rufe suke, saidai ana iya shiga kasar idan ana da sahihan takardu, ko kuma ta sararin sama ko ta iyakokin ruwa.
Saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Abuja.
Facebook Forum