Shugaban Iran, Hassan Rouhani, ya ce, "matsin lambar" da gwamnatin Trump take nunawa kasarsa, bai yi tasiri ba, sannan takunkumin da ta sanya bayan da ta fice daga yarjejeniyar shekarar 2015 kan shirin nukiliyar Iran ya nuna cewa Amurka ta zaku matuka.
Da yake magana kafin tafiya zuwa birnin New York don halartar taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara, Rouhani ya kuma ce, Amurka da Saudiyya sun zuzuta barnar da wani harin da aka kai kan matatun man Saudiyya ya yi a farkon wannan watan.
Sannan ya zargi gwamnatin Trump da burin ganin ya maido da yankin karkashin ikonsa.
Gabanin wadannan kalamai, Shugaba Rouhani tun da farko ya ce shirye-shiryensa akan tarukan Majalisar Dinkin Duniyan, sun hada da gabatar da wasu tsare-tsare da za su tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin.