Dan wasan kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya, Cristiano Ronaldo, ya fadi gaskiya tare da kin yarda da bugun fenariti da alkalin wasa ya ba shi yayin da suke kara wa da kungiyar Persepolis ta kasar Iran a gasar cin kofin zakarun nahiyar Asiya.
Ana cikin fafata wa a wasan ne Ronaldo ya fadi a sashin kusa da ragar Persepolis, lamarin da ya sa alkalin wasa Ma Ning, ya hura fenariti.
Amma nan take Ronaldo ya bi sahun ‘yan wasan Persepolis yana kalubalantar hukuncin alkalin, inda shi da kansa ya fadi gaskiya ya ce ba fenariti ba ce kamar yadda AP ya ruwaito.
Ba da bata lokaci ba, alkalin wasan ya garzaya gefen fili don duba na’ura VAR, ya kuma soke bugun fenaritin bayan bincikensa.
Ita dai Al- Nassr wacce tuni ta yi nasarar shiga zagayen kwaf daya a rukuninsu na E, ta kai wannan mataki ba tare da an yi nasara ko da sau day aba.
Da ‘yan wasa goma kungiyar ta Al-Nassr ta buga wannan wasa wanda aka ta shi 0-0.