Ronaldo Ya Ceci Al-Nassr A Gasar Zakarun Asiya

Ronaldo da abokan wasansa na Al-Nassr suna murnar kwallon da ya zura

Ronaldo ya zura wata kwallo da aka soke saboda an ce ya yi satar gida.

Cristiano Ronaldo ya zura kwallon da ta ba Al-Nassr nasara a karawarsu da Al-Rayyan ta Qatar da ci 2-1 a matakin rukuni na Elite na Gasar Zakarun AFC.

Ronaldo ya zura kwallo da aka soke saboda an ce ya yi satar gida, amma bugunsa cikin saman raga da minti 14 da suka rage a Riyadh ya ba Al-Nassr damar lashe wasan.

Riyad Mahrez ya ci kwallonsa ta farko a kakar wasa yayin da Al-Ahli ta Saudiyya suka ci Al-Wasl na Hadaddiyar Daular Larabawa 2-0 don samun nasara ta biyu a jere.

Al-Sadd ta Qatar ta doke Esteghlal ta Iran da ci 2-0, yayin da abokin hamayyarta ta Tehran, Persepolis, ta tashi kunnen doki 1-1 da Pakhtakor na Uzbekistan.