Tsohon Lauya na musamman da ya yi bincike kan katsalandan din Rasha a zaben Amurka na 2016, Robert Mueller, ya amince zai bayyana a gaban kwamitin da ke kula da fannin shari’a, da kuma kwamitin da ke kula da fannin tattara bayanan sirri na Majalisar Wakilan Amurka domin ya ba da bahasi - a wata mai zuwa.
Shugabannin kwamitocin biyu, Jerrold Nadler da Adam Schiff, sun bayyana a wata wasika a daren jiya Talata cewa, Mueller zai bayyana a gabansu a ranar 17 ga watan Yuli, inda suka kara da cewa, kowa ya zaku ya saurari bahasinsa.
Shi dai Mueller ya kwashe kusan shekaru biyu yana bincike kan katsalandan din da Rasha ta yi a zaben na 2016, da kuma zargin da ake yi cewa Shugaba Trump ya yi yunkurin hana doka ta yi aikinta ta hanyar hana binciken.
Bayan da ya kammala binciken, Mueller ya fitar da wani tacaccen rahoto wanda aka fitar baina jama’a a watan Afrilu, wanda sakamakonsa ya nuna cewa kwamitin yakin neman zaben Trump bai hada kai da Rasha ba a lokacin zaben, amma kuma rahoton bai fitar da matsaya kan ko Shugaba Trump ya yi yunkurin hana doka ta yi aikinta ba.