‘Yan adawa a kasar Venezuela sun ba da sanarwar fara zanga-zangar kwanaki biyu a cikin wannan makon domin tursasa wa shugaba Nicholas Maduro ya soke zaben nan da ya kudiri aniyar yi a ranar 30 ga wannan watan domin zaben ‘yan majalisa.
Masu adawar sun "muna kira ga daukacin jama’ar kasa, da kungiyoyi da su shiga cikin yajin aiki na sa’o’i 48 a ranar laraba da alhamis," kamar yadda dan majalisar dokokin Simon Calzadilla ke cewa.
Calzadilla ya ce zanga-zanga za ta biyo bayan yajin aikin a ranar juma'a inda za a bukaci Maduro da ya soke wannan batun zaben a hukumance.
Sai dai shugaban ya yi kememe duk da karuwar zanga-zangar da ake samu a kasar dama kiraye-kiraye daga sassan duniya daban-daban kan shawo kan rikicin ta hanyar sasantawa da 'yan adawan.