Hukumar ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, ko kafin ayi juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Shugaba Muhammed Bazoum, a karshen watan jiya, kasar ta kiyasta mutanen dake fuskantar matsanancin karancin abinci sama da milyan 3.
Haka kuma mutane sama da milyan 7 da aka dauka a matsayin masu dan dama dama, ga matsalar abincin, a yanzu lamarin su Ka iya baci, sakamakon rikicin da ya kunno kai, kamar yadda hukumar kula da ayyukan jinkan ta Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadi, inda ta yi misali da bayanan Hukumar abinci ta Majalisar.
A ranar 26 ga watan Yuli ne dai wasu dakarun tsaron Shugaban kasa, suka tsare Bazoum mai shekaru 63 a duniya, a juyin mulki na 5 da aka yi a kasar Nijar tun bayan samun ‘yancin kanta daga Faransa, a shekarar 1960.
Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace, tana cigaba da kai taimakon abinci cikin Nijar, duk kuwa da rikicin siyasar dake cigaba da rarakar kasar mai fama da talauci.
A halin da ake ciki kuma, yau Laraba Amurka tace,tana cigaba da bibiyar abin dake faruwa a kasar. Ta ce, Sabuwar Jakadiyar ta a Nijar, Kathleen Gibbon, zata isa birnin Yamai, duk kuwa da juyin mulkin da aka yi a kasar a watan jiya.
Wani jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Amurka yace, ana sa ran isarta Nijar a wani lokacin cikin mako mai zuwa.
A karshen watan jiya ne, jim kadan bayan juyin mulkin, Majalisar Dattawan Amurka ta amince da nadin Kathleen, wadda jami’ar diplomasiyya ce a harkokin kasashen waje, kusan shekara guda da zabarta a mikamin.
Mataimakin mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Vedant Petel ya shaidawa manema labarai cewa, ba wani shirin da aka yi na ta mika takardun ta ga jagororin juyin mulkin, kuma aikin da za ta yi a ofishin jakadancin baya bukatar hakan.
Ya kara da cewa, zata tafi can ne domin jagorantar ofishin jakadancin a yanayi mai wahala, domin mara baya ga alummar Amurkawa, da kula da kokarin da gwamnatin Amurka ke yi.
Your browser doesn’t support HTML5
~Hauwa Sheriff~